Thursday, November 19, 2015

Manyan Labarai Guda 8 A Ranar Laraba

Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 8 wadanda da sukayi fice a ranar Laraba 18 ga watan Nuwamba. Ku duba domin ku same su.




sambo dasuki ii

Kanar Sambo Dasuki



1. Sambo Dasuki Ya Bada Bayanin Shayen Makamai


Kanar Sambo Dasuki yayi bayani akan yadda suka kashe kudaden tsaro da a yadda aka sawo makaman. Ya bayyana cewa anyi hakan ne saboda Najeriya.


2. Matar Tinubu Ta Zauna A Kujerar Ekweremadu



Sanata Oluremi Tinubu ta zauna a kujerar mataimakin shugaban majalisar dattatwa, Ike Ekweremadu wanda hakan ya jaza kace nace.


3. An Fara Shari’ar Nnamdi Kanu



Alkalin kotu mai sauraron karar Nnamdi Kanu ya umurci DSS dasu zo dashi nan gaba idan za’a sake sauraron karar tashi.



4. Wani Dan Najeriya Ya Bukaci A Kulle Ofishin Jakadancin Najeriya



Farfesa Alexia Thomas ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari daga kulle ofishin jakadancin Najeriya dake Ingila. Domin kuwa akwai hadin baki tsakanin hukumar shike da fice Ingila da kuma masu kare iyakar kasar.



5. Tsohon Ministan Ilimi Ya Rasu



Tsohon ministan Ilimi wanda ya role kujerar tsaki 2007-2008, Igwe Aja Nwachukwu ya rasu a Isira’ila.



6. Sojojin Najeriya Sun Lalata Inda Yan Boko Haram Ke Hada Makamai



Sojoji Najeriya sun samu nasarar wargaza inda yan Boko Haram ke hada makamai su.



7.  Harin Bam Guda 2 Ya Kashe Mutane 20 A Kano



Wani harin bam da aka kai a jihar Kano yayi sanadiyyar kashe mutane 20 da kuma raunata mutane masu yawa.



8. Shugaba Buhari Ya Kori Alkali Akanbi Daga Aiki



Shugaba Buhari ya Kori Alkali Lambo Akanbi Wanda aka zargi da amsar cin ha cin Naira Milyan 100.


The post Manyan Labarai Guda 8 A Ranar Laraba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.







Manyan Labarai Guda 8 A Ranar Laraba

About Author

Related Posts

0 Comments: