Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin 14 ga watan Maris, ku duba domin ku same su.
1. An kama wani gwamna a dakin Mata a wata jami’a
Gwamnan Elgeyo Marakwet, an kama shi a dakin mata a cikin wata jami’a
2. Yanayin da Almajirai suke ciki
Jameel ya bar Kebbi ne inda ya hato Kano domin ya zama Malami. Yanzu ya kamalla karatun shi yana da shekaru 17.
3. An shirya bikin nuna kaya a Abuja
An samu baki sosai wadanda suka halarci taron nuna kaya da akayi a Abuja a ranar 12 ga watan Maris.
4. Buhari ya sanya takalman Miliyan 2.5?
Daraktan sababbin hanyoyi sada labarai na jam’iyyar PDP, Deji Adejnayu, ya bayyana cewa takalman da shugaban kasa Buhari ya sanya da zaya tafi Guinea ana saida su kimanin Fam na Ingila Dubu Takwas, wanda yayi kimanin Naira Miliyan Biyu.
5. Shehu Sani ya zargi Elrufai da kokarin ture Buhari a 2019.
“ Ya kamata Elrufai yayi aikin dake gaban shi ba wai kawai ya sanya ma fadar shugaban kasa ido ba”
6. Jonathan ya hadu da tsofaffin Ministocin shi
Saboda cigaba da kame da gwamnatin Buhari keyi akan yaki da rashawa ya sanya tsohon shugabn kasa Jonathan ya hadu da wasu tsofaffin Ministocin shi.
7. Bincike; Najeriya zata iya fuskantar wani sabon yakin basasa
Bincike ya nuna cewa yadda Najeriya ke tafiya yanzu zata iya sake fuskantar akin basasa.
8. Shari’ar Saraki a CCT: Sauka yanzu – Kungiya
Wata kungiya tayi kira ga shugaban majalisar Dattawa daya sauka akan shari’ar da yake fuskanta a kotun CCT
9. Wasu ayoyin Bible masu ban tsoro.
Wani fasto ya fitar da wasu ayoyi a cikin littafin Bible masu ban tsoro sosai.
10. Wuraren da ba’a tabawa idan ana jima’i
Masana halayyar dan dam sun bayyana cewa akwai wurare 5 da ba’a san ana tabawa idan ana jima’i.
The post Manyan Labarai 10 da sukayi fice a ranar Litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Manyan Labarai 10 da sukayi fice a ranar Litinin
0 Comments: