– Zanga-zanga ta barke a garin Jos da safiyar ranar Litinin
– Wannan ya faru ne saboda ana zargin yan banga da kashe matasa 4
– An kona Police station
Rikicin a unguwar Rukuba, Jos
Zanga-zanga ta barke a garin Anguwar Rukuna da safiyar Litinin 14 ga watan Maris. Wannan ya faru ne saboda zargin da ake yima wasu yan banga da kashe mutane 4 a unguwar wadanda basu da laifin komai.
Wata majiya ta bayyana cewa matasa 4 an kashe su ne da daren Lahadi, 13 ga watan Maris. Jaridar Breaking Times ta bayyana cewa wasu matasa da suka fusata sun kona wata police station dake a unguwar domin nuna rashin amincewar su da abunda yan bangar suka aikata a jiyan.
Wata wuta mai ci. Jos
Wasu matasa a Rukuba, Jos
Wannan dai yana daya daga cikin rikicin da garin ya fuskanta tun shigar sabuwar shekara ta 2016.
KU KARANTA: Yan fashi sun farma yar jarida
A shekarun baya Jihar taga rigingimu daya inda ake rikici tsakanin yan asalin jihar da kuma mazauna. Anyi wasu kazamun rigingimu a 2005, wanda ya sanya tsohon shugaban kasa Obasanjo ya cire gwamna Dariye a lokacin.
Haka kuma anyi rikici a 2009 a lokacin mulki mariganyi tsohon shugaban Kasa Ummaru Musa Yar’adua. Jihar ta dade a karkashin dokar ta baci saboda irin rikice-rikicen da ake yi.
The post Jos: Matasa na zanga-zanga saboda kashe yan uwan su 4 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Jos: Matasa na zanga-zanga saboda kashe yan uwan su 4
0 Comments: