– Yan sanda sun cafke matsafa 3 a jihar Ogun
– Matsafan sun addabi kauyukan Oke-Oko da Igborufu na jihar
– An amshe bindiga da sauran makaman dake hannun su
Matsafan da akak kama a Jihar Ogun
Rundunar Yan sandan johar Ogun sunyi nasarar cafke wasu matsafa dake addabar Oke-Oko, Igborufu dake cikin karmar hukumar Sagamun Jihar. An kama su ne da misalin karfe 5 na marece.
KU KARANTA: Yan kasuwar Mile 12 sun koma Ogun
Wadandan aka kama sune; Lekan babatunde, Segun Owodunmi da Musa Ibrahim.
Abubuwan da aka kama daga hannun su sun hada da; Bindiga halba ruga, Harhshi mai yawa, Adda, Layoyi, hotunan wasu daga cikin yan kungiyar da kuma faifai wata mota mai lamba LAGOS VF 117 KJA.
A cewar wata sanarwa daga rundunar yan sanda ta hanyar jami’i mai hudda da jama’a na jihar, DSP Olamuyiwa Adejobi, duka matsafan 3 an kama su ne a wurare dabam dabam.
Sanarwar kuma ta bayyana cewa wani Babatunde Lekan wanda aka kama an kama shine a gidan wani Yusuf Muftau wanda shi ba’a kama shi ba.
DSP Olamuyiwa yace ” Matsafan sun hadu ne a Oke-Oko a wani biki da zasu gudanar na shigar da sabbin mutane cikin kungiyar. Shugaban yan sanda na Ogijo ne ya jagoranci rundunar yan sandan wajen inda aka kama su.
KU KARANTA: Jos: Matasa na zanga-zanga saboda kashe yan’uwan su 4
” Saboda bayanai da yan sanda suke dashi ya sanya aka kama su.
Mutanen yankin sun yaba ma yan sandan sosai inda suka bayyana cewa ” Matsafan sun addabe su kuma sun sanya masu tsoro cikin zukata.
Shugaban Yan Sandan Jihar Abdulmajid Ali ya yaba ma duka wadanda suka taimaka ma yan sanda aka kama matsafan. Kuma ya bayyana cewa za’a tura matsafan zuwa Ofishin SARS dake a Magbon a cikin Jihar.
Shugaban yan sandan kuma yayi kira ga jami’an yan sanda da su cigaba da dage damtse wajen kawo karshen matsafa a jihar. Ali ya bayyana cewa ” Kawo karshen matsafa a jihar shine hanyar da za’a wanzar da zaman lafiya domin matsafa sune ummul kaba’isin duka wata fitin a jihar.”
The post A Ogun: Rundunar Yan sanda ta kama matsafa 3 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
A Ogun: Rundunar Yan sanda ta kama matsafa 3
0 Comments: