Monday, November 9, 2015

Zaben Taraba: Atiku Ya Taya Aisha Alhassan Murna

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya taya Aisha Alhassan murna akan nasarar zaben Tataba data samu a kotu.



atiku abubakar iv

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya



A Wani hoto daya sanya a shafin shi na sada zumunta yace: “Ina alfahari da goya ma Aisha Alhassan baya a lokacin zabe. Yanzu duk wata karamar yarinya dake so ta zama Gwamna ya samu abin kwaikwayo. Muna bukatar mata irin su.”



Idan za’a iya tunawa, kotu ta soke zaben Darius Ishiyaku na jam’iyyar PDP akan zaben 11 ga watan Afirilu da aka yi na jihar, inda ta bayyana Aisha Alhasssan a matsayin Gwamna.



Ishiyaku ya sha alwashin daukaka kara da shi da jam’iyyar shi. Sannan kuma ta zargi shugaban kasa da jam’iyyar APC da hada kai da fannin shari’a wajen murkushe jam’iyyar.  Jam’iyyar APC ta maida martani inda ta bayyana ma PDP ta zargi kanta ba APC ba.


The post Zaben Taraba: Atiku Ya Taya Aisha Alhassan Murna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.









Source: naij.com







Zaben Taraba: Atiku Ya Taya Aisha Alhassan Murna

About Author

Related Posts

0 Comments: