Saturday, October 31, 2015

Manyan Labarai Da Sukayi Fice A Ranar Juma’a

Naij.com ta tattara maku manyan labarai da sukayi fice a ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba. Ku duba domin ku same su.



boko haram iv

Yan ta’addan Boko Haram



1. Wani Bidiyo Ya Nuna Yadda Sojin Najeriya Keyi Ma Yan Boko Haram Tambayoyi 


Wani bidiyo wanda ke yawa ha nuna wani daki cike da wadansu wadanda ake zargin cewa yan Boko Haram. An Nuna su suna nan zanne kasa wani mutum mai rike da kemara yana yi masu tambayoyi.



2. Yan Boko Haram Sun Kai Hari A Bara


Yan kungiyar Boko Haram sun kai wani hari a Lauyan Bara dake karamar hukumar Gulani a jihar Yobe.



3. Bamu Fara Tattaunawa Da Yan Boko Haram Ba – Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ma wani Gidan Talabijin ikon na Indiya cewa, gwamnatin shi bata fara tattaunawa da yan Boko Haram saboda ba’a san suwaye shugabannin su ba.



4. Kotu Ta Yadda CCT Ta Saurari Karar Saraki


Kotun daukaka kara ta kori karar da Bukola Saraki ta kai a korarin hana kotun CCT bincikar shi.



5. Magoya Bayan Biafra Sunyi Zanga Zanga A Hong Kong


Magoyin bayan a ware yan Biafra sunyi zanga zanga a Hong Kong inda suka ringa daga tutar Biafra kuma suk nemi gwamnati data saki Nnamdi Kanu.



6. David Mark Ya Jajanta Ma Iyalan Sanata Gyang


Sanata David Mark ya jajanta ma iyalan Sanata Gyang Pwajok, tsohon dan takarar PDP na jihar Filatu a zaben 2015.



7. Yaushe Buhari Zaya Rantsar Da Ministoci?


Wata majiya ta bayyana lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari yake shirin rantsar da Ministocin shi.



8. Hameed Ali Ya Kori Ma’aikatan Kastam 34


Shugaban hukumar Kastam, Hameed Ali ya amince da kiran mutane 34 daga aikin Kastam. Jami’i mai hudda da Jama’a na Kastam, Wale Adeniyi ne ya bayyana haka.



9. Sarkin Borgu Kitoro Na Ukku Ya Rasu


Sarkin Borgu, Muhammad Bashir Iliyasu ya rasu.



10. An Kai Sarki Sanusi Na Kano Kara A Kotu 


Alhaji Salim Abubakar Bayero ya kai Sarkin Kano kara akan cewa yana son ya ruguza wasu gine-gine a fada domin ya gina ma hakimai Ofisoshi.


The post Manyan Labarai Da Sukayi Fice A Ranar Juma’a appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.









Source: naij.com







Manyan Labarai Da Sukayi Fice A Ranar Juma’a
Previous Post
Next Post

About Author

0 Comments: